Daular Gana
Daular Gana wanda kuma aka fi sani da Ghana, Ghanata, Wagadou, ko Awkar, daular Afirka ta Yamma ce da ke kudu maso gabashin Mauritania da yammacin Mali ta zamani wacce ta wanzu daga Marni 1 zuwa karni 10. Mutanen Soninke ne suka kafa daular, kuma an kafa shi a birnin Koumbi Saleh.